Zanga Zanga: Hankula Sun Tashi Bayan Jami'in Tsaro Ya Harbi Kansa

Publish date: 2024-04-28

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - An samu hargitsi a unguwar Bulumkutu da ke Maiduguri bayan wani jami'in hukumar shige da fice (NIS) ya harbi kansa sau uku a ƙafa.

Jami'in ya yi harbin ne bisa kuskure lokacin da yake aikin tare mutanen da suka fito domin gudanar da zanga-zanga.

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun buɗe wuta yayin da masu zanga zanga suka toshe babban titi a Arewa

Jami'in tsaro ya yi harbi bisa kuskure

Jaridar Leadership ta rahoto cewa ƙarar harbe-harben ya harzuƙa masu zanga-zangar bisa tunanin cewa ɗaya daga cikinsu aka harba, amma hankula sun kwanta bayan sun fahimci abin da ya faru.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Tawagar jami'an tsaron haɗin gwiwa da ta haɗa da ƴan sanda, sojoji, DSS, NIS, NSCDC sun kulle mahaɗar layin dogo ta Bulumkutu domin hana masu zanga-zangar shiga birnin Maiduguri.

Yunkurin tarwatsa 'yan zanga-zanga

Jami’in da ya raunata kansa yana cikin tawagar jami’an tsaro da aka tura domin tarwatsa gungun masu zanga-zangar da suka fito.

Jami’in wanda ba a bayyana sunansa ba, an garzaya da shi asibitin da ke kusa domin yi masa magani, kuma a halin yanzu ba a san halin da yake ciki ba.

Karanta wasu labaran kan zanga-zanga

Kara karanta wannan

'Yan sanda sun sha sabon alwashi kan zanga zanga bayan nasarar gwamnati a kotu

Ƴan sanda sun kora masu zanga-zanga

A wani labarin kuma, kun ji cewa zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a jihar Bauchi ta tarwatse yayin da jami'an ƴan sanda suka watsa barkono mai sa hawaye kan waɗanda suka fito.

Tun farko dai masu zanga-zangar sun taru ne a ƙofar fadar Sarkin Bauchi. inda suka nemi a yi masu iso domin su gana da mai martaba sarki.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

ncG1vNJzZmigkarAonrLnp6irF6jtHC6xLCqaGlmZYJ3fI9msZqml5Z6u63NoJhmoJGjuLa4wGaqrqZdqa60tMhmmZqxkaN6q63MomStq5GnvG7FwGafmqqSnnqsrc2smGg%3D